ALAMOMIN KYAKYKYAWAN KARSHE !! Dr Jamilu Yusuf Zarewa
*_Tambaya_*

Assalam Alaikum !
Dan Allah me ake nufi da kyakyawan qarshe, akwai wasu sifofin da siga na mutuwa da yake nuna cewa in sha Allah mutum yayi kyakyawan Qarshe??


*_Amsa_*

Wa alaikum assalam,
Akwai alamomin da yawa da suke nuna kyakykyawan karshe daga ciki akwai:

*1*.Cikawa da Kalmar Shahada, saboda fadin Annabi (SAW) "Duk Wanda maganarsa ta karshe ta zama La'ilaha illallahu zai Shiga aljanna".

*2*.Mutum ya mutu yana aikin alheri kamar sallah Hajji,  saboda fadin Annabi SAW " Ana tashin bawa akan abin da ya mutu yana yi".

*3*. Idan mutum ya rasu Daren juma'a ko yininta saboda fadin Annabi SAW "Duk Wanda ya rasu Daren juma'a ko yininta Allah zai kare shi daga azabar Kabari"

*4*. Idan mutum ya yi shahada kamar mace ta mutu wajan haihuwa ko ciwon ciki ko nutsewa a ruwa ko ya mutu a ciwon Kwalara ko kare kansa ko dukiyarsa DSS

*5*.Idan mutum ya rasu yana gumin goshi kamar yadda ya tabbata a hadisin Tirmizi .

Allah ne mafi sani

*_Dr. Jamilu Zarewa_*

28/07/2018

Share this


0 comments:

Post a Comment