KA BA NI DON ALFARMAR ANNABI !! Dr Jamilu Yusuf Zarewa


Tambaya
Assalamu Alaikum Dr.
Malam wanda suke cewa ku ba ni don alfarmar manzon Allah suma be kamata su dinga fadi ba?

Amsa
Wa alaikum assalam Akwai sabanin malamai akan haka, amma mafi yawan malamai suna ganin ana neman tsani ne da abubuwa uku kacal:

*1.* Ayyuka nagari, kamar ya ce: ka ba ni da son Annabi.
*2.* Neman tsani da Allah ko daya daga cikin siffofinsa.
*3.* Addu'ar mutumin kirki.
Wadannan abubuwa guda uku su ne ingantattun nassoshi suka tabbatar ana neman tsani da su.
Wanda ya nemi tsani da alfarmar Annabi ba za'a ce ya yi shirka ba, sannan bidiantar da shi yana da wahala saboda akwai riwaya daga Imamu Ahmad wacce take halatta fadin hakan, kamar yadda Sheik Sa'ady Wanda ya rasu a (1393) ya ambata a littafinsa Majmu'ul Fawa'id.

Allah ne mafi sani

Amsawa

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
30/07/2018

Share this


0 comments:

Post a Comment