FIFITA TSAKANIN KISHIYOYI HARAMUN NE !!!Dr Jamilu Yusuf ZarewaTambaya

Assalamu Alaikum.
Malam na kasance  inna kyautata  Ma mijina  iya gwargwadona, to amma matsalan  ba ni kade bace sai  yakasan ce  nima yana mun duk wani Abu najin dadi da kyautatawa fiye da kishiyar tawa wani Lokacimma  baya Boyewa to shin malam bama Shiga hakkinta. Menene hukuncin haka.
Nagode


*Amsa*

Wa alaikum assalam
Ya wajaba ayi adalci a lamura na zahiri (kamar abinci, tufa) tsakanin kishiyoyi, Annabi SAW yana cewa: "Duk Wanda yake da mata biyu, amma bai yi adalci a tsakaninsu ba, zai zo ranar alkiyama sahensa daya a shagide".
Ya halatta in kana da mata guda biyu ka fi son daya daga ciki, ka fi jin dadin saduwa da ita, ka fi dadewa a dakinta, Annabi SAW ya fi son nana Aisha akan duka matansa tara da ya mutu ya bari, kuma  matansa da sahabbansa sun san hakan, kamar yadda ya tabbata a sahihul Bukhari.

Allah ne mafi sani

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

12/08/2018


Share this


0 comments:

Post a Comment