IDAN AKA SAMU RIKITA-RIKITA A WAJAN SAKI, ZUWA KOTU SHI NE MAFITA !! Dr Jamilu Yusuf Zarewa
Tambaya

Assalamu'Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuh! Don Allah Mallam ina fatawa akan batun Auren yarinyar da Mijinta suka samu matsala har ta kai ga ta koma gida akan cewa ba ta son shi.
A takaice dai mijin da yaje gidan su, ya tambayeta akan 'yanzu me take so'? Sai tace masa ita rabuwa take so su yi, Sai yace mata to kije mun rabu, Kuma gobe kafin karfe 10 na safe ki zo ki kwashe kayanki, Kuma ki bada 'yata a kawo min, Sai ta ce da shi ai a rubuce ake yi, sai yace mata, ai sanda aka daura auren ba'a ce ya rubuta ba, saboda haka yanzu ma ba sai ya rubuta ba. Bayan anyi haka, sunje  kwashe kaya sai yace ai shi bai ce ya sake ta ba. Har sai da lamarin ya kai ta matsa masa akan takardar, sai ya rubuta cewa" Ni wane na saki matata saki daya, amma na maida ita"
 Mallam sai tace masa ai ba'a rubuta haka Saidai ya rubuta sakin kawai.. amma maidawar Sai ya zo daga baya a furuci kawai. Sai ya karbi wannan takardar ya yaga ya sake rubuta wata, cewa yayi saki daya, a bisa sharadin in yayi hakan za ta koma? Tace da shi za ta koma. To amma bayan ya rubuta sai Ta ce ita wallahi ba zata koma ba. Shi kuma mijin yace ya maida ta, ita kuma ta ce wallahi ba za ta komaba koda ko zata mutu ne.
Malam tace ita aurenshi ya zamo mata wani abin al'ajabi don ba ta taba jin sonsa a ranta ba ko da da kwayar zarra ne a  ranta. saboda munanan halayensa sun sa ba ta iya yi masa biyayya ko kadan. Kuma tace ba zata taba iya yin hakan ba. Don haka sai take ganin hanyar halaka ce suka kama dukkansu. Don haka ita bazata iya komawa ba, Shi kuma yace halayensa da basu da kyau babu wanda ya isa yasa shi ya canza, koda ko mahaifiyar sa ce da mahaifin sa, malam yana neman mata, da tayi magana sai yace mata wallahi yanzu ya soma. Wai meyasa iyayenta ba su yi bincikeba tun farko, suka daura musu auren?

Don Allah Malam menene mafita anan? Yanzu haka saboda bakin cikin lamarin , tana nan a kwance ba lafiya.

*_Amsa_*
Wa alaikumus salam
Sakin mace da baki yana daidai da sakinta a rubuce, magana ma tafi rubutu karfi a shariance, don haka ta saku tun furuncinsa na farko.

Idan miji ya saki matarsa saki daya yana da damar da zai mata kome mutukar ba ta gama idda ba, kuma iyayen matar ko ita kanta ba su da damar da za su ja masa birki kamar yadda aya ta (228) a suratul Bakara ta tabbatar da hakan.

Idan bangaren amarya da Ango suka jaa daaga aka kasa samun matsaya, zuwa kotu shi ne maslaha, fatawa ba za ta yi tasiri ba, saboda alkali yana da karfin hukuma, malami kuma aikinsa bada hukuncin Allah kawai, wannan yasa nake baku shawarar zuwa kotu don ta warware muku rikicin da kuke ciki.

Ya halatta mace ta nemi saki idan ya zamanto akwai cutarwa tsakaninta da mijinta ko kuma ba za ta iya tsayawa da hakkokinsa ba, kamar yadda kissar Thabit bn Kais bn Shammas da matarsa Jamila ta tabbatar da hakan a hadisai ingantattu.

Allah ne mafi sani

*_Dr. Jamilu Zarewa_*

12/09/2018

Share this


0 comments:

Post a Comment