FATAWAR RABON GADO (180) Dr Jamilu Yusuf Zarewa
Tambaya

Assalamu alaikum Malam Yayanmu ya mutu ya bar ni da Kanina da Kanwata da muke Uwa daya, uba daya, sai kuma matansa guda biyu, ya bar (320,000) yaya rabon zai kasance ?

Amsa

Wa alaikum assalam To dan'uwa kai da kaninka kowa za'a ba shi (96,000) kanwarku kuma za'a bata (48,000) kowacce daga cikin matansa za'a bata (40,000).

Allah ne mafi sani

Amsawa✍🏻

DR.JAMILU YUSUF ZAREWA

27/09/2018

Share this


0 comments:

Post a Comment