FATAWAR RABON GADO(182) Dr Jamilu Yusuf Zarewa


*Tambaya*

Assalamu alaikum malam Ahsanallahu ilaikum
Mutum ne ya rasu ya bar magada kamar haka:
Mata daya
Shakikai biyar (Maza biyu Mata uku)
Li-Abbai bakwai (Maza biyar Mata biyu)
Li-Ummiyya daya.
Ahsanallahu ilaikum yaya za a raba gadonsu?

*Amsa*

Wa alaikum assalam, Za'a raba gida (12), a bawa matarsa kashi uku (Rubu'i), a bawa li'ummiya kashi biyu (Sudus), ragowar kashi bakwan sai a bawa shakikai su raba, duk namiji ya dau rabon mata biyu.

Allah ne mafi sani

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
02/10/2018

Share this


0 comments:

Post a Comment