FATAWAR RABON GADO(183) Dr Jamilu Yusuf Zarewa


*Tambaya*

Assalamu alaikum malam Allah Ya kare ma na ku Ya kara mu ku basira. Ga tambaya kamar haka: Mace ce ta rasu ta bar 'ya mace guda daya da 'yan uwa shakikai guda uku mata daya na miji. Ta bar kudi naira 73,900. Ya ya gadonta zai kasance? Allah Ya saka da alheri.

*Amsa*

Wa alaikum assalam, za'a bawa 'Yar rabin dukiyar (36,950), kowacce 'yar'uwa mace za'a bata (7,390), shi kuma namijin za'a ba shi (14,780).
Allah ne mafi sani

*Amsawa*✍🏻
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
03/10/2018

Share this


0 comments:

Post a Comment