HUKUNCIN HULDA DA KRISTOCI!! Dr Jamilu Yusuf ZarewaTambaya

Assalaamu alaikum.
Allah ya qarawa Dakta lafiya, don Allah ina son amsar tambayoyin nan tare da hujja don gamsar da abokan karatuna.
1. Minene matsayin amsa gayyatar chiristoci zuwa cikin choci don wani taro da suke yi na graduation ko makamancin haka amma a cikin choci?
2. Minene matsayin shiga choci din karan-kansa?
3. Menene matsayin fara yiwa wanda ba musulmi ba sallama ?

Allah ya qarawa mallam ikhlasi da ilimi mai amfani

*Amsa*

Wa alaikum assalam, Annabi (SAW) ya hana fara yiwa CRISTER sallama kamar yadda ya zo a hadisin Tirmizi.

Ya halatta Musulmi ya yi hulda da Crister ya kuma kyautata masa in har ana zaune lafiya , kamar yadda aya ta (8) a suratul Mumtahanah ta tabbatar da hakan, sannan zai iya cin yankansa kamar yadda aya ta (5) a suratul Ma'idah ta yi bayanin hakan.
Annabi (SAW) ya rasu silkensa na yaki yana wajan Bayahude, saboda ya amshi abincin da za'a ci a gidansa, sannan da aka bude Khaibar ya bar gonakin musulmai a wajan Yadudawa sun rinka nomawa suna bawa musulmai wani kaso kamar yadda Bukhari ya rawaito a Sahihinsa

Nasaran Najran sun zo wajan Annabi SAW ya sauke su a Masallaci, sannan   ya  zo a Musannaf a lamba ta: (4871) cewa: " Sahabin manzon Allah Abu-Musa Al'ash'ary ya taba yin sallah a wata coci da ake cewa NAHYA a Damshk lokacin da bai samu  masallacin ba.

Tarurrukan Kristoci ba sa rabuwa da kade-kade da raye-raye da cakuduwa tsakanin maza da mata, ga kuma manyan hotuna a like a bango, wannan yasa rashin halartar taronsu shi ne daidai, saboda gujewa keta iyakokin Allah.

Allah ne mafi sani

*Dr. Jamilu Zarewa*

13/09/2018

Share this


0 comments:

Post a Comment