Fatawar Rabon Gado (186) - Dr Jamilu Yusuf Zarewa


*Tambaya*

ASSALAMU ALAIKUM MALAM MUTUM NE YA RASU YA BAR MAGADA KAMAR HAKA:
AKWAI UWA AKWAI MATAN AURE BIYU AKWAI DIYA (MAZA UKU) MATA (GOMA SHA BIYU) KUMA KUDI NE ZA A RABA MUSU NAIRA DUBU TALATIN DA UKU.

*Amsa*

Wa alaikum assalam Za'a bawa Mahaifiyarsa (5500) matansa biyu kuma za'a ba su (4125) su raba, ragowar (23375) sai a bawa Diyansa su rabe a tsakaninsu, duk namiji ya dau rabon mata biyu.

Allaha ne mafi sani

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF  ZAREWA*

05/10/2018

Share this


0 comments:

Post a Comment