HUKUMCIN SHAN MAGANIN TAURI ! Dr Jamilu Yusuf Zarewa


 
Tambaya

Assalamu alaikum Allah ya karawa Dr. Lafiya.
Mene ne hukuncin shan maganin tauri wato Maganin karfe ko kauranci a musulunci ?

  Amsa
Wa alaikum assalam
Mutukar babu abin da ya sabawa sharia a ciki, ana iya amfani da shi saboda neman kariya,  saboda duk mua'amalolin da mutane suke yi, in har ba'a samu nassin da ya haramta ba, to sun halatta saboda Ka'idar: الأصل في الأشياء الإباحة.

Da yawa daga cikin magungunan tauri akwai kauce hanya a ciki, akwai wadanda ake barin sallah idan an sha, ka da aje garin-neman-gira a-rasa- IDO.
Mutukar maganin tauri ya kunshi abin da sharia ta haramta, bai halatta ayi amfani da shi ba, Biyayya ga Allah maganin KAU-DA-BARA.

Amsawa✍🏻
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
25/03/1440
03/12/2018

Share this


0 comments:

Post a Comment