FITINA A KWANCE TAKE, ALLAH YA LA'ANCI MAI TADA ITA ! - Dr Jamilu Yusuf Zarewa*Tambaya*

Assalamu alaikum. malam ina da tambaya hadisin da yake magana akan fitina tana barci duk Wanda ya tashe ta Allah Yana tsine masa. Hadisin ya inganta ko a'a ? Kuma a Wani littafi da Shafi yake?

*Amsa*

Wa'alaikum salam
tabbas mai Kanzul -ummal da kuma mai jami'ussagir sun rawaito shi a matsayin hadisi, saidai Albani ya raunana shi a Dha'iful jami'i da kuma Silsilatil-ahdithil- dha'ifah a 7\259, saboda a cikin sanadin hadisin akwai mutanen da ba'a san su ba.

Allah ne mafi sani.

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

2/1/2014

Share this


0 comments:

Post a Comment