FATAWAN RABON GADO (193) - Dr Jamilu Yusuf Zarewa
*Tambaya*

Assalamu Alaikum
Mallam  tambaya ta akan  rabon gado ne.
Mutum ne ya mutu,ba Mata,ba yaya,ba iyaye sai kakarsa wacce ta haifi mahaifinsa da Dan uwa wadda  suke uba daya sai wadanda suke uwa daya. To mallam ya rabon gadonsa zai kasance?
Hafizakallah.


*Amsa*

Wa alaikum assalam , za'a raba gida (6), a bawa  kakarsa kashi daya, 'yan uwan da suka hada uwa kashi biyu, ragowar sai a bawa dan'uwansa li'abbi.

Allah ne mafi sani

*Dr. Jamilu Yusuf Zarewa*

06/01/2019

Share this


0 comments:

Post a Comment